Tankar mai ta yi karo da motocin ‘yan kasuwa a hanyar Lokoja zuwa Abuja

Wata tankar mai ɗauke da man fetur ta fashe bayan wani hatsarin mota da ya auku a hanyar Lokoja zuwa Abuja a jihar Kogi.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa direban motar na jigilar man ne zuwa wata unguwa a jihar, sai motar ta ƙwace, ya rasa yadda zai yi da ita, ya je ya yi karo da wasu motocin.

An gano cewa fashewar ta faru ne sakamakon illar da hatsarin ya yi, kuma gobarar da ta tashi ta ƙone tankar mai, da wasu motoci tare da wasu mutane da suka maƙale a ciki.

Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, ba a iya tantance adadin mutanen da suka maƙale a cikin motocin ba.

KU KUMA KARANTA: Hatsarin mota ya ci rayukan mutane 14, ya jikkata 5 a Bauchi

Sai dai jami’an agajin gaggawa da suka haɗa da jami’an hukumar kiyaye haɗura ta tarayya (FRSC) sun mamaye wurin domin ceto lamarin tare da fara aikin ceto.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kwamandan hukumar FRSC na jihar, Stephen Dawlung, ya ce hatsarin ya haifar da koma-baya ga ababen hawa a kan hanyar.

Ya kuma lura da cewa mutane da dama da abin ya shafa sun maƙale ne a cikin motocin sun kasa fita.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *