Bayan dakatar da tattara sakamakon zaɓen Adamawa, ‘yar takarar jam’iyyar APC, Sanata Aisha Binani Ɗahiru, ta shigar da ƙara a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda ta buƙaci a sake duba hukuncin da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta yanke (INEC) a ranar 16 ga Afrilu dangane da ayyana ta a matsayin wadda ta lashe zaɓen gwamna.
Idan ba a manta ba INEC ta dakatar da tattara sakamakon zaɓen bayan da kwamishinan zaɓe na jihar Adamawa Hudu Yunusa ya sanar da Aisha Binani a matsayin wadda ta lashe zaɓen yayin da ake ci gaba da ƙidayar ƙuri’u.
A cikin aikace-aikacenta, Sanata Binani tana kuma neman umarnin haramtawa INEC da jami’anta ɗaukar duk wani mataki na bayyana wanda ya lashe zaɓen har sai an tantance buƙatar ta na neman a sake duba shari’a.
KU KUMA KARANTA: INEC ku sanar da Fintiri a matsayin wanda lashe zaɓen gwamnan Adamawa – PDP
‘News Point Nigeria’ ta sami kwafin aikace-aikacen da aka kawo bisa ga Dokoki na 34 na 1a, oda 3(1) & 3(2) a, b, c, Order 6 na Babban Kotun Tarayya (Dokokin Farar Hula) 2019 da Sashe 251 (1)q & r na Kundin Tsarin Mulki na 1999, da kuma Sashe na 149 & 152 na Dokar Zaɓe na 2022.
A dalilin shigar da takardar, Sanatan ya bayyana cewa bayan tattara sakamakon zaɓe, INEC (wanda ta kai ƙara a matsayin wanda ake ƙara na farko) ta bayyana ta a matsayin wacce ta lashe zaɓen amma jam’iyyar PDP da ɗan takararta.
Gwamna Ahmadu Fintiri wanda aka shigar da ƙara a matsayin masu amsa na 2 & 3 ya koma faɗa tare da tayar da hankulan jama’a wanda ya kai ga duka ga ma’aikatan INEC. Wannan rikicin, inji ta, ya sa INEC ta soke sanarwar farko da ba ta da hurumin yi domin kotun sauraren ƙararrakin zaɓe ce kaɗai ke da irin wannan iko.
Da soke sanarwar ta, Sanata Binani ta ce INEC ta ƙwace ikon kotun sauraron ƙararrakin zaɓe wadda ita ce kotu ɗaya tilo da ke da hurumin bayyana gudanar da zaɓe. A cikin takardun da ta gabatar a gaban kotun, Sanata Binani ta bakin lauyoyinta ƙarkashin jagorancin babban Lauyan Najeriya, Hussaini Zakariyau, ta ce akwai batun sake duba shari’a don baiwa kotun ƙoli damar tantance ayyuka da hukunce-hukuncen kotunan ƙananan hukumomi da kuma ɓangaren majalisa da gudanarwa na gwamnati ciki har da hukumomi da jami’an gwamnati.
Ya ƙara da cewa hukumar ta INEC kasancewarta hukumar gwamnati za ta iya tantance ayyukanta da bayananta da hukunce-hukuncen da kotu ta yanke kuma kotu ce kaɗai za ta iya soke ayyukan jami’in INEC ba ita kanta INEC ba.
Neptune Prime ta rawaito cewa Hudu Yunusa Ari, wanda ya ayyana Binani a matsayin wanda ta lashe zaɓen ba bisa ƙa’ida ba, INEC ta dakatar da kwamishinan zaɓe (REC) da sanyin safiyar ranar Litinin.
INEC ta fitar da wata wasiƙa zuwa ga REC na Adamawa inda ta umarce shi da ya ƙaurace wa ofisoshin hukumar nan take har sai an sanar da shi.
[…] KU KUMA KARANTA: Ta maka INEC da PDP a kotu kan zargin ayyana ta a matsayin zaɓaɓɓiyar gwamnan Adamawa – Binani […]
[…] KU KUMA KARANTA: Ta maka INEC da PDP a kotu kan zargin ayyana ta a matsayin zaɓaɓɓiyar gwamnan Adamawa – Binani […]