Suna Rokon Gwamnain Zamfara Da Ta Koma Da ‘Ya’yansu Makaranta

0
497

Daga Wakilinmu

Yayin da ake komawa makarantu a faɗin Nijeriya a ranar Litinin, wasu iyayen yara a Zamfara mai fama da hare-haren ‘yan fashin daji sun koka a kan rashin buɗe makarantun da su.

Sun ce rashin komawa makarantun ‘ya’yansu a safiyar yau, alama ce da ke nuna cewa dubban ‘ya’yan talakawa a jihar za su ci gaba da zaman gida tsawon zangon karatu na biyu ke nan.

Gwamnatin Zamfara dai ta rufe makarantun jihar ne a farkon watan Satumba, bayan sace gomman ɗalibai daga Sakandiren Ƙaya a cikin ƙaramar hukumar Muradun da yammacin ranar wata Laraba.

Wani uba ya shaida wa BBC cewa suna tsaka mai wuya; ”Muna kira ga gwamnatin jihar Zamfara ta duba girman Allah ta bude mana makarantun yara, wannan matsalar tsaro wadda ita ce aka ce ta janyo rufe makarantun ba wai Zamfara kadai ta shafa ba, shin don me a nan za a mayar tamkar nan ne gidan matsalar?

An rufe makarantu tun watan Agustan bara, watanni biyar kenan, kuma babu wata magana guda. An yi Term guda yara na zaman gida, yanzu duk inda za a koma makaranta ban da namu ‘ya’yan. Kowancan Term guda da aka yi wasu daga cikin mutanenmu da sun san ba za a koma makarantar ba da tuni sun dauki mataki,” in ji shi.

Ya kara da cewa kwata-kwata ma ba a batun komawar ‘ya’yan na su makaranta, an rubutawa gwamnati rahoto kan cewa akwai rukuni uku na makarantu a jihar Zamfara, wato launin ruwan Dorawa (Yellow), da launin Kore (Green) da kuma launin Ja (Red).

  • Rukunin Ja, sam karatun ba zai yiwu ba saboda garuruwan su na hannun ‘yan bindiga.
  • Su kuma launin ruwan Dorawa su na da dan dama-dama, ana iya yin karatun amma kuma za a ba su kariya.
  • Sai kuma launin Kore, sam ba su da wata matsala, domin makarantun a cikin gari suke.

Uban ya kara da cewa wannan matsala ta kin bude makarantun ta janyo mutane da dama su na yi mata kallo na daban, don haka su na kara kira ga gwamnati ta sake duba lamarin domin ‘ya’yansu su samu komawa makaranta.

BBC ta tuntuɓi kwamishiniyar Ilmi ta jihar Zamfara, Hajiya Lawal Gummi a kan wannan batu da kuma zarge-zargen da ake yi, sai dai ta ce a yanzu ba za su yi wani ƙarin haske ba.

Ko da yake, wasu iyayen da ba su yarda mu naɗi muryoyinsu ba, sun ce sun samu masaniyar cewa gwamnati na nan tana kammala tsare-tsaren da suka wajaba don ganin an ci gaba da karatu a jihar nan ba da daɗewa ba.

Leave a Reply