Suluhu ta lashe zaɓen shugaban ƙasar Tanzaniya yayin da ake ci gaba da tashin hankali a ƙasar

0
226
Suluhu ta lashe zaɓen shugaban ƙasar Tanzaniya yayin da ake ci gaba da tashin hankali a ƙasar
Shugabar Tanzania Suluhu

Suluhu ta lashe zaɓen shugaban ƙasar Tanzaniya yayin da ake ci gaba da tashin hankali a ƙasar

Hukumar zabe ta kasar Tanzaniya ta bayyana Shugaba Samia Suluhu Hassan a matsayin wadda ta lashe zaben shugaban kasa da aka yi takaddama a kai, inda ta samu kusan kashi 98 cikin 100 na kuri’un da aka kada.

Sai dai zaben ya haddasa tarzoma da tashin hankali a sassan kasar, inda jam’iyyar adawa ta Chadema ta ce sama da mutane 700 ne suka mutu. Kakakin jam’iyyar, John Kitoka, ya bayyana cewa mutanen da suka rasu sun fi yawa a biranen Dar es Salaam da Mwanza, kuma adadin na iya karuwa saboda dokar hana fita da gwamnati ta kafa.

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta tabbatar da cewa ta samu bayanai game da kisan akalla mutane 100, yayin da majiyar tsaro ta fada wa AFP cewa adadin na iya kaiwa tsakanin 700 zuwa 800.

Kitoka ya zargi gwamnati da “ci gaba da kisan masu zanga-zanga,” tare da neman kafa gwamnati na rikon kwarya domin shirya sahihin zabe. Sai dai gwamnatin Tanzaniya ta musanta adadin mutanen da aka kashe, tana mai cewa rahotannin sun yi nesa da gaskiya.

Shugabar Tanzania ta kori wasu ministocinta daga aiki

Ministan harkokin wajen kasar, Mahmoud Thabit Kombo, ya ce jami’an tsaro ba su yi amfani da karfi fiye da kima ba, inda ya bayyana abubuwan da suka faru a matsayin “kananan rikice-rikice” da ’yan ta’adda suka haddasa.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya bukaci gudanar da bincike mai zaman kansa kan zargin amfani da karfi da yawa.

Suluhu, wadda ta karbi mulki a 2021 bayan rasuwar tsohon shugaban kasa John Magufuli, tana neman wa’adinta na farko cikakke a karkashin jam’iyyar Chama Cha Mapinduzi (CCM). Amma rashin manyan ’yan adawa a zaben, da aka hana shiga ko aka tsare, ya jefa shakku kan sahihancin zaben.

Leave a Reply