Sojojin Sudan sun kai farmaƙi birnin Khartoum
Harin an kai shi ne a kan dakarun sa kai na RSF, a wani mataki na farmaƙin Soja mafi girma tun bayan ɓarkewar rikicin.
Wasu majiyoyi daga cikin sojojin Sudan da shaidun gani da ido, sun ce rundunar sojan Sudan ta ƙaddamar da wani farmaƙi da sanyin safiyar ranar Alkhamis a Khartoum, babban birnin ƙasar Sudan,.
Harin an kai shi ne a kan dakarun sa kai na RSF, a wani mataki na farmakin soja mafi girma tun bayan barkewar rikicin.
KU KUMA KARANTA:MƊD ta bayyana damuwa kan ƙaruwar tashin hankali a Sudan
Rahotanni daga birnin na Khartoum sun nuna na cewa sojojin sun auna sansanonin dakarun RSF da ke babban birnin kasar da hare-hare ta sama da manyan bindigogi.
Kunigyar ‘yan tawayen na RSF suna rike da ikon kusan dukkanin babban birnin kasar tun bayan da rikicin ya barke a watan Afrilun 2023 tsakanin hafsan hafsoshin sojojin Sudan Janar Abdel Fattah Burhan da kwamandan dakarun RSF Mahamed Hamdan Dagalo.
Janar-janar din biyu da a yanzu ba sa ga maciji, a da baya, sun taba zama abokan kawance a gwamnatin rikon kwaryar Sudan, bayan juyin mulkin 2021, amma sun zama abokan hamayya saboda mulki.