Rundunar sojin sama ta Najeriya ta ce ta halaka gomman ‘yan ta’adda a wani hari da ta kai tsaunin Mandara, inda ta ce ta kawar da wasu daga cikin manyan ‘yan ƙungiyar.
Sojojin sama na Operation Haɗin Kai ne suka kai wannan harin a ranar Juma’a, 24 ga watan Nuwambar 2023, inda sojojin suka ce wannan samamen nasu na daga cikin mafi nasara a tarihin rundunar ta Operation Haɗin Kai.
A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojin sama Edward Gabkwet ya fitar, sojojin sun kai wa ‘yan ta’addan hari a yayin da ‘yan ta’addan suka taru a kusa da wasu gidaje uku masu rufin kwano waɗanda bishiyoyi suka zagaye su.
“Daga bidiyon da aka ɗauka, da alama ‘yan ta’addan sun taru ne a wurin domin gudanar da wata tattauna da suka shirya ko kuma shirya wani babban hari.
KU KUMA KARANTA: Sojoji sun damƙe waɗanda ke kai wa Bello Turji makamamai a Zamfara
“Sama da ‘yan ta’adda 100 ɗauke da muggan makamai ne aka gansu suna ta mu’amula da juna tare da shawagi a kusa da gine-ginen waɗanda a kusa da su akwai motoci huɗu na ɗaukar soji,” in ji sanarwar.
Rundunar sojin ta ce bayan samamen da dakarunta suka kai sun gano cewa dakarun nata sun lalata gine-gine biyu cikin uku da ke wurin sannan an lalata motocin ‘yan ta’addan baki ɗaya.
“Haka kuma akwai alamun Abu Asad, wanda babba ne a ƙungiyar Ali Ngulde da ke ƙarƙashin Boko Haram da sauran ‘yan ta’adda kamar Ibrahim Nakeeb da Mujaheed Dimtu da Mustafa Munzir da sauran mayaƙa duk suna daga cikin ‘ya ta’addan da aka kashe a harin.”
Arewa Maso Gabashin Najeriya na daga cikin yankunan kasar da ke fama da rikicin ‘yan ta’addan Boko Haram, duk da cewa jami’an tsaron ƙasar na cewa suna samun nasara kan ‘yan ta’addan.
Domin ko a cikin wannan watan na Nuwamba sai Hedkwatar Tsaro ta Nijeriya (DHQ) ta ce dakarun ƙasar sun kashe ’yan ƙungiyar Boko Haram/ISWAP da sauran ‘yan bindiga 113 kuma sun kama mutum 300 bayan wasu jerin farmaki da suka kai ɓangarori dama na ƙasar a cikin mako ɗaya.