Dakarun tsaron Najeriya sun kashe gomman masu tayar da ƙayar baya da suka haɗa da manyan kwamandojin ƙungiyar ISWAP, a yankin arewacin ƙasar, kamar yadda rundunar soji ta bayyana a ranar Talata.
Rundunar sojin sama ta Najeriya ce ta kai hare-haren sama a maɓoyar mayaƙan ƙungiyar a kusa da Tafkin Chadi a jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar.
ISWAP ita ce ƙungiyar da ta ɓalle daga Boko Haram. Ta daɗe tana ayyukan ta’addanci a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi, inda ta kashe dubban fararen hula da jami’an tsaro, tare da raba miliyoyin mutane da muhallansu.
“Hare-haren sun yi matuƙar taimakawa wajen rage ƙarfin ƙungiyar a yankin,” kamar yadda rundunar sojin saman Najeriya ta faɗa a cikin wata sanarwa.
An kai hare-haren a ƙauyen Kolleram ne tun a ranar Asabar, amma ba a sanar wa al’umma ba sai a ranar Talata.
KU KUMA KARANTA: Mutum 3 sun rasu, an jikkata 10 a rikicin sojoji da ’yan Keke NAPEP a Yobe
Aƙalla masu tayar da ƙayar baya 30 aka kashe, ciki har da manyan kwamandojin ƙungiyar, Ali Dawud da Bakura Fallujah da Mallam Ari, in ji rundunar sojin.
“Waɗannan hare-haren suna nuna irin muhimmin ci gaban da ake samu na yaƙi da ta’addanci a Najeriya,” a cewar sanarwar.
Hare-haren sun lalata wani muhimmin waje da ƙungiyar ke amfani da shi wajen ayyukan samar da abinci,” sanarwar ta faɗa.