Sojojin Najeriya sun ceto mutane 214 da kuma kashe ‘yan ta’adda da dama a mako 1

0
109
Sojojin Najeriya sun ceto mutane 214 da kuma kashe 'yan ta'adda da dama a mako 1

Sojojin Najeriya sun ceto mutane 214 da kuma kashe ‘yan ta’adda da dama a mako 1

Daga Ali Sanni

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa a cikin makon jiya dakarunta sun kashe ‘yan ta’adda 108 sannan sun ceto mutum 214 da aka yi garkuwa da su a kasar.

Jami’in yada labarai na rundunar Edward Buba ya sanar da hakan a Abuja ranar Juma’a.

Buba ya ce jami’an tsaron sun kama ‘yan ta’adda 204 sannan sun ƙwato makamai 66 da harsasai 4,087.

Ya ƙara da cewa sauran abubuwan da dakarun suka kama sun hada da rediyo ƙirar HH, motoci 19, baburan 44, wayoyin hannu 3 da kuɗi naira miliyan 4.9.

A Arewa maso Gabas dakarun dake aiki a ƙarƙashin ‘Operation Hadin Kai’ sun kashe mahara 47, sun kama wasu 18, sun ceto mutum 130 da aka yi garkuwa da su sannan sun ƙwato makamai da dama.

Buba ya ce a cikin makon ‘yan ta’adda tare da iyalen su 622, mata 182, maza 90 da yara kanana 350 suka miƙa wuya ahannun jami’an tsaron.

Rundunar sojin sama dake aiki a ƙarƙashin ‘Operation Hadin Kai’ a ranar 2 ga Agusta sun yi wa wata sabuwar maɓoyar Boko Haram/ISWAP da wurin da suke haɗa bamabamai dake tsaunin Mandara luguden wuta inda suka kashe mahara da dama.

Buba ya ce a Arewa ta Tsakiya rundunar ‘Operation Safe Haven’ da ‘Whirl Stroke’ sun kashe mahara 13, sun kama wasu 57 sannan sun ceto mutum 36 da aka yi garkuwa da su.

KU KUMA KARANTA;UNDP ta buƙaci inganta haɗin kan sojoji da fararen hula a yankunan da ake fama da rikici

A Arewa maso Yamma jami’an tsaron dake aiki a karkashin rundunar ‘Operation Hadarin Daji’ sun kashe ‘yan ta’adda 15, sun kama wasu 22 sannan sun ceto wasu mutane har 27 da aka yi garkuwa da su a jihohin Kaduna, Katsina, Sokoto da Zamfara.

Ya ce rundunar sojin sama dake ƙarƙashin rundunar sun kashe mahara da dama a harin da suka kai a maɓoyar ‘yan bindiga Kamilu Burazu a ƙananan hukumomin Danmusa da Batsari dake jihar Katsina.

Buba ya ce rundunar ‘Operation Whirl Punch’ sun kashe mahara 8, sun kama wasu 22 sannan sun ceto mutum 12 da aka yi garkuwa da su a jihohin Kaduna, Neja da Kogi.

Dakarun sun ragargazza maɓoyar ‘yan bindiga a ƙaramar hukumar Giwa dake jihar Kaduna.

A Kudu maso Kudu Buba ya ce rundunar ‘Operation Delta Safe’ sun kama lita miliyan 1.13 na danyen mai, AGO lita 228,770, DPK lita 100 da lita 20,000 na PMS.

Ya ce dakarun sun ragargaza rijiyoyin mai 487, jiragen ruwa 34, manyan tankuna 12, murhun dafa abinci 71, da sauransu.

Dakarun sun Kuma kama motoci 19, babura 32, Keke NAPEP daya sannan sun ragargaza matatun mai 76.

Buba ya ce dakarun sun ceto mutum biyar da aka yi garkuwa da su, sun kama ɓarayin man fetur 32 da bindigogi da harsasai 11.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here