Wasu matuƙan jirgi biyu na rundunar sojin saman Najeriya (NAF) sun tsallake rijiya da baya a hatsarin da ya rutsa da su yayin da dawowa daga atisayen da suka saba yi.
A cewar daraktan hulɗa da jama’a na rundunar sojin, Air Vice Marshal Edward Gabkwet, hatsarin ya afku ne a kimanin tazarar mil 3.5 daga filin jirgin saman sojin da ke Kaduna.
Lamarin dai ya faru ne da misalin karfe 2:35 na ranar Alhamis a kusa da filin sauƙar jiragen sama na sojoji a garin Kaduna.
Sanarwar ta ce hukumomin sojin saman sun ba da umarnin gudanar da bincike na farko don gano musabbabin hatsarin jirgin.
KU KUMA KARANTA: Mutum 6 sun rasu, 11 sun jikkata a hatsarin mota a Ebonyi
Hatsarin dai ya biyo bayan wani jirgin sama mai saukar ungulu kirar MI-35P na sojin saman Najeriya da ya faɗo a cikin watan Disamba, kuma shi ne karo na uku da ya afku tun watan Yuli.