Sojoji sun sanar da Janar Nguema a matsayin shugaban ƙasar Gabon

2
490

Daga Ibraheem El-Tafseer

Jagororin sojin da suka yi juyin mulki a Gabon sun sanar da Janar Brice Oligui Nguema a matsayin shugaban ƙasar na riƙon-ƙwarya.

Lamarin na faruwa ne ‘yan awanni bayan wasu sojoji daga rundunar tsaron fadar shugaban ƙasa sun zagaya da shi a titunan birnin Libreville don yin murna.

Ɗazu Shugaba Ali Bongo ya saki wani saƙon bidiyo daga gidan da ake tsare da shi, yana neman abokansa su ƙyamaci juyin mulkin, yayin da mutane ke ci gaba da murna a titunan ƙasar.

KU KUMA KARANTA: Da ɗumi-ɗumi: Sojoji sun yi juyin Mulki a ƙasar Gabon

Shi da mahaifinsa sun mulki ƙasar da ke da arziƙin man fetur tsawon shekara 56, amma da yawan ‘yan ƙasar na zaune cikin talauci.

2 COMMENTS

Leave a Reply