Sojoji sun lalata matatun mai da ba sa bisa ƙa’ida, sun kama mutane 42 a cikin makonni uku

Hedikwatar Tsaro, (DHQ) ta ce dakarun haɗin gwiwa na Operations ‘DELTA SAFE’ sun gano tare da lalata wuraren tace mai ta haramtacciyar hanya guda 30 tare da kama masu zagon ƙasa 42 a cikin ayyukan makwanni uku.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wani taƙaitaccen rubutu na ayyukan yaɗa labarai na tsaro wanda Birgediya Janar Abdullahi Ibrahim ya karanta kan ayyukan sojojin da ya gudana tsakanin 15 ga Yuni zuwa 6 ga Yuli 2023.

Ya ce sojojin a ƙoƙarinsu na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali na harkokin kasuwanci a shiyyar Kudu maso Kudu na ƙasar sun gudanar da sintiri, kai samame, kwasar fadama da kuma yaƙi da haramtacciyar hanyar satar man fetur a rafuka, magudanar ruwa, manyan tekuna hanyoyin garuruwa da garuruwan Delta, Bayelsa, Ribas da Jihar Cross Ribas.

KU KUMA KARANTA: Dakarun Najeriya sun kai samame sansanonin ‘yan fashin mai, sun kama da dama

Ya ce an gudanar da ayyukan ne da nufin hana masu aikata laifuka ‘yancin yin aiki. Sakamakon haka, sojojin sun gano tare da lalata wuraren tace mai ba bisa ƙa’ida ba 30, tankunan ajiya 125, tanda 227, ramuka 11 da kwale-kwalen katako guda 21.

Sojojin sun kuma ƙwato litar ɗanyen mai lita 1,675,700, lita 74,500 na Man Fetur, Motoci 10, Babura 20, Makamai 8 da alburusai iri-iri 330 yayin da aka kama masu zagon ƙasa 42 a cikin wa’adin da aka ɗiba.

Ya ce an miƙa duk wasu kayayyakin da aka kwato da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa da aka kama, an miƙa su ga hukumar da ta dace domin ɗaukar mataki.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *