Sojoji sun kama masu ƙera haramtattun makamai a Filato

0
171

Sojoji sun bankaɗo wata masana’antar ƙera makamai ta bayan fage a yankin Vom da ke ƙaramar hukumar Jos ta kudu a jihar Filato.

“An kuma kama wasu mutum biyu da ke haɗa bindigogin suke kuma safararsu ,” in ji kakakin rundunar soji ta Operation Safe, Kyaftin Oya James.

Ya bayyana cewa a yayin samamen, sojojin sun kama bindigogi 6 ƙirar AK-47, SMG 4 da  kuma pistol a haramtacciyar masana’antar makaman.

Sauran haramtattun makaman sun haɗa da bodin bindigogi ƙirar AK; kayan badin bindigogi, kwanson albarusai, jigidan harsasai da kuma kayan ƙiran bindigogi.

Leave a Reply