Sojoji sun hallaka riƙaƙƙen ɗan ta’adda, Halilu Sububu a Zamfara

0
38

Sojoji sun hallaka riƙaƙƙen ɗan ta’adda, Halilu Sububu a Zamfara

Rahotanni daga jihar Zamfara na nuni da cewa sojojin Najeriya sun hallaka Halilu Sububu, ɗan ta’adda da ya yi ƙaurin suna a yankin Arewa maso Yamma.

Sububu, wanda ya kwashe shekaru yana ta’addanci a jihar Zamfara, ya gamu da ajalinsa a ranar Alhamis.

Wata majiyar asiri ta tsaro a safiyar yau Juma’a ta tabbatar da kisan dan ta’addan da sojoji su ka ga jaridar PRNigeria.

KU KUMA KARANTA:Rundunar sojojin ruwan Najeriya ta bankaɗo wata runduna ta bogi da ke yi mata Sojan Gona

“A wani samame da dakarun soji suka kai jiya, sun yi nasarar hallaka shahararren dan bindigar nan Halilu Sububu tare da wasu ‘yan bindiga da dama a Zamfara a daren jiya.

“Sojoji sun kuma kwato muggan bindigogi da alburusai, tare da babura daga hannun ‘yan ta’adda,” in ji majiyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here