Sojoji sun fatattaki ‘yan bindiga uku a Mangu, sun ƙwato makamai

Dakarun runduna ta 3 ta Najeriya da aka tura domin kwantar da rikicin ƙaramar hukumar Mangu da ke jihar Filato, a ranar Larabar da ta gabata sun kashe wasu ‘yan bindiga uku a yankin baki ɗaya.

Daraktan hulɗa da jama’a na rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a Abuja.

Mista Nwachukwu ya ce sojojin sun kashe masu laifin ne a lokacin da suka yi artabu ta hanyar kwanton ɓauna da ‘yan bindigar suka yi, a lokacin da suke amsa ƙiran gaggawa a yankin Mangu.

KU KUMA KARANTA: Yan bindiga sun kashe mutane tara tare da ƙona gidaje shida a yankin Filato

Ya ce sojojin sun ƙwato bindigu ƙirar AK 47 guda uku, harsasai 14 na masu tsayin mita 7.62 na musamman, babur ɗaya da kuma katin shaidar ‘yan sanda na Constabulary bayan sun yi nasarar fatattakar ‘yan kwanton ɓaunar.

A cewarsa, a halin yanzu sojoji suna bin ‘yan bindigar da suka tsere da raunukan harbin bindiga a yayin musayar wuta.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *