Sojoji sun damƙe waɗanda ke kai wa Bello Turji makamamai a Zamfara

0
235

Rundunar soji ta sanar da cewa, a wani samame daban-daban da dakarunta suka gudanar sun kama wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne da ke kai wa wani ɗan bindigan nan mai suna Bello Turji makamai.

Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja a ranar Alhamis, 23 ga watan Nuwamba, 2023, Daraktan ayyukan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Edward Buba, ya ce wadanda ake zargin suna kan hanyarsu ta kai wa shugaban ‘yan bindigar Zamfara makamai da alburusai ne a lokacin da sojoji suka kama su.  .

Mutanen uku da sojoji ba su bayyana sunayensu ba, an kama su ne a Kaduna a wani samame da aka gudanar tsakanin ranakun 14 zuwa 17 ga watan Nuwamba, 2023.

Hedikwatar tsaro ta bayyana a ranar 14 ga Nuwamba, 2022, ta bayyana Turji da wasu 18 da ake nema ruwa a jallo tare da ba su kyautar N95m ga wanda ya bada labarin inda za a kama su.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Zamfara ta ba da umarnin rufe kasuwar Maru, bayan harin ‘yan bindiga a garin

An yi la’akari da shi a matsayin ɗaya daga cikin manyan ‘yan bindiga, Turji na da hannu a zargin kisan mutane kusan 200 da suka haɗa da mata da yara a watan Janairun 2022.

An kuma ce shi ne ya kai harin a ƙauyen Garki da ke Sokoto, inda aka kashe sama da mutane 80 a cikin dare a shekarar 2021.

Leave a Reply