Sojoji sun damƙe riƙaƙƙen ɗan ta’adda, sun kuɓutar da mutanen da ya yi garkuwa dasu

0
60
Sojoji sun damƙe riƙaƙƙen ɗan ta’adda, sun kuɓutar da mutanen da ya yi garkuwa dasu

Sojoji sun damƙe riƙaƙƙen ɗan ta’adda, sun kuɓutar da mutanen da ya yi garkuwa dasu

A saƙon da ta wallafa a shafinta na X a ranar juma’a, rundunar sojin na ci gaba da kai zafafan hare-hare akan ‘yan ta’adda a ko’ina a faɗin Najeriya.

Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewar dakarunta sun kama wani riƙaƙƙen ɗan ta’adda da aka jima ana nema, Hussein Usman, a ƙauyen Ganawuri, dake ƙaramar hukumar Riyom ta jihar Filato tare da kuɓutar da mutanen da yake garkuwa dasu.

Rundunar ta ƙara da cewa dakarunta sun kuma ƙwace makamai da sauran muhimman kayayyakin da ‘yan ta’addar ke amfani dasu, inda ta ƙara tsaurara matakan da take ɗauka akan ɓatagarin dake ɓoye a cikin dazuzzuka.

KU KUMA KARANTA:Mun kashe ’yan boko haram 5, 44 sun miƙa wuya – Sojojin Najeriya

A cewar rundunar, bayan samun sahihan bayanan sirri a ranar 11 ga watan Satumbar da muke ciki, dakarunta dake jihar Filato sun yi nasarar kama dan ta’addar da aka jima ana nema, Usman Hussein, wanda ya bayyana cewa shine yake kitsa munanan hare-haren da ake kaiwa a jihar Filato.

A yau ne rahotanni daga jihar Zamfara suka tabbatar da nasarar hallaka kasurgumin dan bindiga nan Halilu Sububu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here