Sojin saman Najeriya sun yi kuskuren kashe mutum 16

0
40
Sojin saman Najeriya sun yi kuskuren kashe mutum 16

Sojin saman Najeriya sun yi kuskuren kashe mutum 16

Sojojin Saman Najeriya sun yi kuskuren kashe fararen hula 16 a yankin Zurmi da ke Maradun a Jihar Zamfara yayin da suke kai wa ’yan bindiga farmaki.

Rahotanni sun nuna cewa mafi yawan waɗanda aka kashe ’yan sa-kai ne da ke yaƙi da ’yan bindiga.

Bayanai sun ce ’yan sa-kai sun nemi taimakon sojojin sama wajen murƙushe ’yan bindigar da suke faɗa da su, amma sojojin sun yi kuskuren ɗaukar su a matsayin ’yan bindiga, tare da kai musu hari.

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya aike da saƙon jajensa ga iyalai da ’yan uwan waɗanda suka mutu.

A gefe guda yaba wa ƙoƙarin sojojin wajen yaƙi da ’yan bindiga a jihar.

Sanarwar gwamnatin jihar ta miƙa ta’aziyya ga ’yan sa-kai na Tungar Kara a Ƙaramar Hukumar Zurmi, waɗanda suka jajirce wajen kare al’umma daga barazanar ’yan bindiga.

KU KUMA KARANTA: Babu wani kuskure a harin jirgin sama a Sakkwato; Janar Musa

Rahotanni sun ce ’yan sa-kai na kan hanyarsu ta barin Gidan Makera a yankin Boko lokacin da harin ya faru, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar 16 daga cikinsu.

Wannan lamari na zuwa ne makonni bayan da wasu ’yan sa-kai sama da 30 suka rasa ransu a Jihar Katsina sakamakon harin ’yan bindiga.

Masana sun danganta irin waɗannan kuskuren ga rashin isasshen musayar bayanai tsakanin ’yan sa-kai da jami’an tsaro, wanda ke haifar da mummunan sakamako a kan fararen hula.

Leave a Reply