Shugabannin Nijar, Mali da Burkina Faso sun kafa ƙungiyar haɗaka
Hukumomin sojan Nijar, Mali da Burkina Faso sun yi bikin raba gari da sauran ƙasashen yammacin Afirka a ranar Asabar, yayin da suka rattaɓa hannu kan wata yarjejeniya ta kafa wata ƙungiya a tsakaninsu.
Taron farko na ƙasashen uku, waɗanda dukkaninsu suka fice daga ƙungiyar ECOWAS a farkon wannan shekarar, an kuma buƙaci a ƙara yin haɗin gwiwa a ɓangarori da dama.
“Mutanenmu sun juya baya ga ƙungiyar ECOWAS ba tare da wata tangarɗa ba,” in ji Janar Abdourahamane Tiani mai mulkin Jamhuriyar Nijar, ya shaidawa ‘yan’uwansa masu faɗa a ji a yankin Sahel a wajen buɗe taron da aka yi a Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar.
KU KUMA KARANTA:ECOWAS na shirin ƙaddamar da kuɗin bai ɗaya da zai yi aiki a ƙasashen ƙungiyar
Shugabannin ukun da suka karɓi mulki ta hanyar juyin mulki a shekarun baya-bayan nan, sun yanke shawarar ɗaukar wani mataki na ƙara samun haɗin kai, tare da amincewa da yarjejeniyar kafa ƙungiyar, a wata sanarwa da suka fitar a ƙarshen taron.
Ƙungiyar ƙasashen yankin Sahel da za ta yi amfani da sunan AES kuma za ta kasance ƙarƙashin jagorancin ƙasar Mali a shekara ta farko, adadin ya kai kimanin mutane miliyan 72.