Shugabannin Afrika na ci gaba da aika wa Trump saƙon taya murna

0
22
Shugabannin Afrika na ci gaba da aika wa Trump saƙon taya murna

Shugabannin Afrika na ci gaba da aika wa Trump saƙon taya murna

Tsohon Shugaban Amurka Donald Trump, wanda ya kasance dan takarar Jam’iyyar Republican a zaɓukan 5 ga watan Nuwamba ya sake samun wani wa’adin a matsayin shugaban kasa, kamar yadda sakamakon zaɓen ke nunawa ranar Laraba.

Ana buƙatar aƙalla ƙuri’un 270 na wakilai masu kaɗa ƙuri’u daga jihohi kafin a ayyana mutum a matsayin wanda ya lashe zaɓen, yayin kafafen watsa labaran Amurka ke hasashen cewa Trump ya samu sama da kuri’u 270 fiye da Mataimakiyar Shugaban Ƙasa Kamala Harris ƴar takarar Jam’iyyar Democratic.
Ba a bayyana sakamakon zaɓen a hukumance ba tukunna.

Trump, wanda ya kasance shugaban Amurka na 45 daga shekarar 2017 zuwa 2021, ya bayyana a jawabinsa a Florida ranar Laraba cewa ya “shawo kan matsalolin da kowa ke tunanin ba zai iya tsallakewa ba”.

Wakilai masu ƙuri’u daga jihohi za su haɗu cikin watan Disamba don tabbatar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa. Za a rantsar da sabon shugaban Amurka ranar 20 ga watan Janairun shekarar 2025.

Wasu shugabannin Afirka sun taya Trump mai shekara 78, murnar lashe zaɓen.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce shugabancin Trump zai sa “ƙasashen biyu su haɓaka haɗin kai ta fuskar tattalin arziƙi da zaman lafiya da kuma magance matsalolin duniya da ke fuskantar mutanenmu.” Tinubu ya ƙara cewa komawar Trump fadar White House “zai shigo da wani zamani mai amfani na cuɗanyar tattalin arziƙi da ci-gaba tsakanin Afirka da Amurka.”

Shugaban Somalia, Shugaba Hassan Sheikh Mohamud ya bayyana zaɓen Trump a “mai cike da tarihi”, yana mai ƙarawa da cewa a wani sakon da ya wallafa a shafin X ranar Laraba cewa: “Ina fatan ci gaba da aiki tare da ƙasashenmu biyu ke yi wajen wanzuwar zaman lafiya da tsaro da kuma bunƙasar tattalin arzikin ƙasashenmu.”

Shugaban Burundi Shugaba Evariste Ndayishimiye ma ya taya Trump murna yana mai cewa: “Ina fatan karfafa alaƙa tsakanin Burundi da Amurka.”

Ƙasar Kongo
Shugaba Felix Tshisekedi na Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo ya bayyawa a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X cewa a shirye yake “domin haɗa kai da sabon shugaban Amurkan da aka zaɓa zurfafa haɗin kan tsakanin Kongo da Amurka waɗanda suke kyakkyawar alaƙa tun a da.”

KU KUMA KARANTA: Zaɓen Amurka: Trump da Harris na buƙatar zage damtse don samun nasara a jihar Georgia

Shugaban Zambia Hakainde Hichilema, a saƙonsa na shafin X ya ce zaɓen Trump “mai cike da tarihi ya nuna ƴancin mutane na zaɓi shugabanninsu “, yana mai ƙarawa da cewa Zambia na fatan “ƙarfafa haɗinkai tare da zumuncinmu” da Amurka.

A saƙonsa na taya murna ga Trump, Shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya ce: “Duniya na buƙatar ƙarin shugabanni masu magana a madadin mutane.

Zimbabwe a shirye take ta yi aiki tare da kai da kuma mutanen Amurka domin gina duniya da ya fi ci-gaba da zaman lafiya.”

Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya ce ƙasarsa tana fatan “ci gaba da haɗin-gwiwa mai amfanar juna” da Amurka.

Ramaphosa ya ƙara da cewa: “A fagen siyasar duniya, muna fatan cewa shugabancinmu ƙungiyar G20 a shekarar 2025, inda za mu yi aiki kut-da-kut da Amurka wadda za ta gaje mu a shugabancin G20 a shekarar 2026.”

A jawabinsa da ya walafa a shafin X Shugaban Masar Abdelfattah El-sisi ya ce “Ina taya zaɓaɓɓen shugaban Amurka Donald Trump murna tare da yi masa fatan alkhairi wajen cim ma burin Amurkawa.”

Sisi ya ƙara da cewa ƙasarsa na fatan ” kasancewa tare wajen samar da tabbatar da zaman lafiya tare da tabbatar da zaman lafiya na yanki da kuma ƙarfafa alaƙa ta musamman tsakanin Masar da Amuka da kuma mutanensu masu ƙaunar juna.”

Shugaban Ethiopia
Abiy Ahmed shi ma a shafinsa na X ya ce : “Ina taya Shugaba Donald Trump murna kan nasararka da kuma komawarka mulki. Ina fatan aiki tare da kai domin ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasashenmu biyu a lokacin mulkinka.”

Ƙarfafa alaƙa’ – Sudan
Shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya ta Sudan Abdel Fattah al-Burhan a saƙonsa na X shi ma ya ce: “Ina taya Shugaba Donald Trump murna kan nasarar da ya samu a zaɓen shugaban ƙasa. Ina kuma faran haɓaka dangantaka tsakanin ƙasarsa da tamu don cin moriyar juna.”

Leave a Reply