Daga Ibraheem El-Tafseer
Shugaban jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, Sanata Abdullahi Adamu ya ajiye muƙaminsa bayan kwashe shekara ɗaya da ‘yan watanni yana jagorantar jam’iyyar.
Sabon shugaban riƙo na jam’iyyar, Sanata Abubakar Kyari ne ya tabbabar da murabus ɗin Abdullahi Adamu, kwana ɗaya bayan kafafen yaɗa labarai a Najeriya sun wallafa rahotanni cewa rashin jituwa tsakanin shugaban na APC da gwamnatin Bola Tinubu ne ya tursasa masa sauƙa daga kujerarsa.
Kwamitin gudanarwa na APC ɗin a zamansa na ranar Litinin ya kuma amince da naɗa Sanata Abubakar Kyari wanda shi ne mataimakin shugaban jam’iyyar a ɓangaren arewacin Najeriya a matsayin sabon shugaban riƙo na jam’iyyar.
A watan Maris ɗin 2022 ne aka zaɓi Abdullahi Adamu a matsayin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa bayan gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya yi shugaban riƙo na kusan shekaru biyu.