Shugaban ƙasa ya taya ‘yan Najeriya murna a saƙonsa na bikin Kirsimeti

0
13
Shugaban ƙasa ya taya ‘yan Najeriya murna a saƙonsa na bikin Kirsimeti

Shugaban ƙasa ya taya ‘yan Najeriya murna a saƙonsa na bikin Kirsimeti

Shugaba Bola Tinubu ya taya ‘yan Najeriya murnar bikin kirsimeti, inda yace kasar tana kan tafarkin sake farfadowa da samun bunkasa.

Shugaban ƙasar a cikin sanarwar dashi da kansa ya rattabawa hannu a yau Talata ya buƙaci al’ummar Najeriya su yiwa shugabannin ƙasar addu’a a kowane mataki.

“A wannan rana ta farin cikin bikin Kirsimeti, ina mika sakon gaisuwata ga ilahirin Kiristocin dake faɗin Najeriya dama duniya baki daya a yayin da muke murnar haihuwar Isa Almasihu, kamar yadda aka bada labari a litattafai masu tsarki,” a cewar Tinubu.

“Najeriya na kan tafarkin farfadowa da samun cigaba, inda dukkanin alamu ke nuna cewar akwai haske anan gaba. a wannan lokaci na bukukuwa, ya kamata su sabunta fata tare da kara samun yakini a kasar najeriya mai yalwar arziki.

KU KUMA KARANTA: Jami’an NSCDC 3,542 ne za su kula da wuraren bukukuwan kirsimeti da murnar sabuwar shekara a Kano

“Ya kamata mu mika irin wadannan sakonnin goyon baya da addu’o’i ga shugabannin kasarmu. da goyon bayanku ne, zamu hidimtawa ƙasarmu yadda ya dace tare da ƙara zabura wajen samun yalwatuwar arziki.”

Ga Tinubu, Kirsimeti na nufin cikar alƙawarin Allah tare da tabbatar da nasarar halayen kauna da zaman lafiya da haɗin kan al’umma.

A cewarsa, bikin wata alama ce mai karfi ta cewar haske na iya bayyana a lokaci mafi duhu, hakan zai wanzar da kwanciyar hankali da kyakkyawan fata, inda ya kara da cewar dukkanin addinai sun yi amanna da hakan. Tabbas, Allah yana tare da mu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here