Shugaban ƙasa bai naɗa jakadu ba – Gwamnatin Tarayya

0
29
Shugaban ƙasa bai naɗa jakadu ba - Gwamnatin Tarayya

Shugaban ƙasa bai naɗa jakadu ba – Gwamnatin Tarayya

Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya tace har yanzu Shugaba Bola Tinubu bai naɗa jakadu ba.

Ma’aikatar na martani ne ga wani jerin sunaye da ake yaɗawa a ƙafafen sada zumunta na mutanen da Shugaba Tinubu ya nada a matsayin jakadun Najeriya a ƙasashen duniya daban-daban.

A sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi mai riƙon muƙamin kakakin ma’aikatar, Kimiebi Imomotimi Ebienfa, ya buƙaci al’umma da suyi watsi da jerin sunayen.

“Da kakkausar murya, ma’aikatar ke bayyana cewa naɗin jakadu hurumi ne na shugaban ƙasa, kuma bai nada kowa,” a cewar Ebienfa.

KU KUMA KARANTA:Muna ƙira da a tallafa wa ci gaban matasa; Gwamnatin Tarayya (Hotuna)

A watan Satumban 2023, Tinubu ya janye dukkanin jakadun Najeriya dake aiki a ƙasashen duniya daban-daban.

Leave a Reply