Sheyi Tinubu, ya yi buɗa-baki da ɗan gidan gwamnan Kano
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Ɗan Shugaban Ƙasa, Seyi Tinubu, ya yi buda-baki tare da Musulmai a Kano, ciki har da Al- Amin Abba Kabir, ɗan gidan gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf a ranar Litinin din data gabata.
Sheyi ya kuma kaddamar da shirin ciyar da marasa galihu da nakasassu a wani bangare na shirinsa na Renewed Hope Youth Engagement (RHYE) a masallacin Al-Furqan dake cikin birnin Kano.
KU KUMA KARANTA:Dokoki 5 da masu wa’azi za su mayar da hankali kansu a watan Ramadan – Majalisar Malamai
Shugaban kasar ya kai ziyara gidan fitaccen dan kasuwan nan, Aminu Dantata, daga bisani kuma ya kai gaisuwar ban girma ga gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf.
Taron buda-bakin na musamman ya samu halartar ba ‘yan jam’iyyar APC kadai ba, har ma na jam’iyyar NNPP, karkashin jagorancin shugabanta na jiha, Hashim Sulaiman Dungurawa.









