Shettima ya jagoranci taron majalisar tattalin arziƙin ƙasa

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya jagoranci taron majalisar tattalin arziƙin ƙasa (NEC), a fadar shugaban ƙasa dake Abuja.

Taron wanda aka gudanar a zauren majalisar dokokin jihar a ranar Alhamis, shi ne na farko tun bayan rantsar da gwamnatin shugaba Bola Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu.

Mataimakin shugaban ƙasa, bisa tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya, shi ne shugaban hukumar.

Taron na NEC, wanda ake gudanarwa duk wata, yana tattaunawa ne kan daidaita ayyukan tsare-tsaren tattalin arziƙi da shirye-shiryen tattalin arziƙi na matakai daban-daban na gwamnati.

KU KUMA KARANTA: An yiwa kalamai na gurguwar fahimta – Kashim Shettima

Majalisar ta ƙunshi gwamnonin jihohi 36, gwamnan babban bankin Najeriya, ministan kuɗi, sakataren gwamnatin tarayya da sauran jami’an gwamnati da hukumomin da ayyukansu ya shafi tattalin arziƙi.

Gwamnonin da tsofaffin ‘yan majalisar sun haɗa da Charles Soludo na Anambra, Yahaya Bello na Kogi, Seyi Makinde na Oyo, Duoye Diri na Bayelsa, Babajide Sanwo-Olu na Legas da Godwin Obaseki na jihar Edo.

Sauran sun haɗa da Umaru Fintiri na Adamawa, Inuwa Yahaya na Gombe, Bala Mohammed na Bauchi, Babagana Zulum na Borno, Hope Uzodinma na Imo, Rotimi Akeredolu na Ondo, Abdullahi Sule na Nasarawa, Mai Mala Buni na Yobe da Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara.

Haka kuma sabbin zaɓaɓɓun gwamnonin sun halarci taron.

A baya dai shugaba Tinubu ya ƙaddamar da majalisar kafin ta ci gaba da taron ta.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *