Shekara 3 bayan ya yi wa ‘yar shekara 4 fyaɗe, kotu ta yanke mishi hukunci

0
212

Babbar kotun jihar Bauchi mai lamba 6 ta yanke hukuncin ɗaurin rai da rai ga Yusuf Bako, mai shekaru 50, bisa samunsa da laifin yi wa wata yarinya ‘yar shekara 4 fyaɗe a cikin wani masallaci da ke kan titin Aminu a cikin birnin Bauchi.

LIB ta ruwaito cewa Bako ya yaudari ƙaramar yarinya zuwa masallaci kuma ya yi mata fyaɗe a cikin Satumba 2020, yayin da ake ci gaba da kullen COVID-19.

A baya dai an ɗaure Bako sau biyu bisa laifukan fyaɗe makamantan haka amma gwamnan jihar ya yi masa afuwa watanni kaɗan domin rage cunkoso a gidajen yari da kuma daƙile yaɗuwar cutar Coronavirus.

KU KUMA KARANTA: Yadda mutum huɗu suka yi wa Yarinya fyade saboda laifin babanta

Darakta mai gabatar da ƙara na ma’aikatar shari’a ta jihar Bauchi Barista Sha’awanatu Yusuf, ta tabbatar da hukuncin a wata hira ta musamman da manema labarai a ranar Laraba 27 ga watan Disamba, 2023.

Ta ce mai shari’a Sa’ad Zadawa na babbar kotu mai lamba 6 ne ya yanke hukuncin a ƙarshen watan Nuwamban wannan shekara bayan sauraron ƙarar daga ɓangarorin biyu.

Sha’awanatu ta bayyana cewa wannan hukunci na nuni da ƙudurin ma’aikatar wajen tabbatar da adalci ga waɗanda aka yi wa fyaɗe da kuma tabbatar da ingancin dokar VAPP da ke aiki a jihar.

Bugu da ƙari, Daraktan ta buƙaci hukumar shari’a ta ƙasa da ta gaggauta gudanar da shari’ar waɗanda ake zargi da aikata laifukan fyaɗe a jihar, tare da sa ran za a ci gaba da hukunta masu laifi.

Ta yi ƙira ga iyaye da masu kula da su da su haɗa kai da hukumomi wajen gurfanar da waɗanda ake zargi da aikata laifin fyaɗe.

“Wasu iyaye suna hana ‘ya’yansu, waɗanda aka yiwa fyaɗe, fitowa a gaban kotu don ba da shaida,” in ji Sha’awanatu.

Abin lura a nan shi ne, a shekarar 2022, Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed, ya amince da dokar VAPP, wadda ta tanadi hukuncin kisa da daurin rai da rai ga waɗanda ake tuhuma da laifin fyaɗe.

Leave a Reply