Sheikh Muhajjadina ya nemi gwamnati ta gaggauta ɗaukar mataki kan tsadar rayuwa

0
151

A daidai lokacin da al’umma Najeriya ke fama da hauhawar farashin kayyakin abinci da tsadar rayuwa, sanannen malamin addinin nan na Jihar Kano, Sheikh Mujajjadina Sani Kano, wanda kuma shi ne Shugaban Masu Ilimin Taurari na Afirka, ya yi ƙira ga shugabanni a dukkan matakan gwamnati da su gaggauta ɗaukar matakin kawo wa mutane sauƙin matsin rayuwar da suke fuskanta in har suna son kauce wa fushin Allah (SWT).

Sheikh Muhajjadina ya yi wannan bayanin ne a hirarsa da manema labarai a garin Kano ranar Talata. Ya kuma ƙara da cewa, halin da mutaten ke ciki da matsin rayuwa ya wuce duk yadda ake tunani. “Lamarin a halin yanzu ya kai matsayin Innalillahi Wa Inna Ilaihi Rajiun”.

Ya ce, babu wani ɓangare na rayuwar al’umma da ba su dandan wannan halin da ake ciki. A kan haka malaman addini musulmunci dana addinin Kirista suka haɗu a yin ƙira ga gwamnati ta samar wa al’umma mafita.

Shehin Malamin wanda shi ne kuma shugaban Gidauniyar (Muhajjadina Humanitarian Foundation) wadda ta shahara wajen tallafa wa al’umma, ya ƙara da cewa, a kullum suna samun mutane masu neman taimako maza da mata da marayu masu lalulori daban-daban., “ Yanzu kusan kowa ka gani a hanya yana buƙatar taimako” in ji shi.

Ya kuma ce, mataki mai muhimmanci da ya kamata gwamnati ta ɗauka don kawo ƙarshen matsalar tsadar rayuwa shi ne dawo da tallafin man fetur da wannan gwamnatin ta janye a farkon kama mulkinta. Ya ce, man fetur ya shafi dukkan ɓangarorin rayuwar al’umma, janye shi ya haifar da tsadar rayuwa. Kuma gashi darajar naira na kara karyewa a kullum, “In har gwamnati ta dawo da wadannan abubuwan biyu to da yardar Allah abubuwa za su yi sauki” in ji shi.

KU KUMA KARANTA: Sheikh Muhajjadina ya yi Allah wadai da harin sojoji kan masu Mauludi a Kaduna

Daga nan Shekih Muhajjadina ya yi gargaɗin cewa, in har gwamnati ba ta ɗauki matakin kawo wa al’umma sauƙin rayuwa ba, to lallai za su gamu da fushin Allah (SWT). “Allah na iya ƙwace mulkin ya ba waɗanda za su taimaka wa mutane” in ji shi.

Ya kuma nemi gwamnati a dukkan mataki su nemi shawarwarin malaman addini wajen gudanar da harkokinsu, musamman abin da ya shafi raba wa al’umma tallafi, “Domin daga cikin malamai ne ake da tabbacin samun masu tsoron Allah, waɗanda za su jagoranci raba wa mutane abin da aka tanada, ya kuma kamata a cire duk wani na’u’i na siyasa a wajen bayar da tallafi, domin yunwa bata san banbanci a tsakanin ‘yan APC ko ‘yan PDP ba” in ji shi.

Leave a Reply