Shaikh Zakzaky ya raba kayayyakin abinci ga mabuƙata a Zariya
Daga Idris Umar Zariya
Kamar yadda aka saba duk shekara a lokacin gabatowar watan azumin Ramadana, na raba kayayyakin abinci ga mabuƙata, a bana ma jagoran Harkar Musulunci a Najeriya, wanda aka fi sani da (‘yan Shi’a), Shaikh Ibraheem Zakzaky ya yi rabon kayayyakin abinci a Zariya da ma wasu garuruwa. A inda za a ci gaba da wannan rabo har cikin azumin Ramadan na bana.
KU KUMA KARANTA:Karyewar Farashin Kayan Abinci: Ba mu shigo da kayan abinci daga waje ba — Minista
Rabon kayan abincin na ranar Talata 26 ga watan Sha’aban 1446 daidai da 25 ga watan Fabarairun din 2025 an soma gudanar da shi ne da misalin ƙarfe 9 na safe. Kayayyakin abincin da aka raba sun haɗa da; gero, masara, shinkafa da sauran su.
Mutane da yawa sun yi yabo ga shaihin malamin dare da yin addu’a gareshi bisa ga wannan ƙokari da yake yi.