Shahararren jarumin wasan kwaikwayo na hausa, Usman Baba Fategi wanda aka fi sani da Samanja ya rasu.
Jarumin ya rasu ne da sanyin safiyar yau, a asibitin lambun garin Kaduna bayan ya sha fama da rashin lafiya.
KU KUMA KARANTA: Fitaccen Malamin addinin Musulunci Sheikh Dokta Yusuf Ali ya rasu
Ya kasance sojan Najeriya mai ritaya kuma ya yi aiki da gidan rediyon tarayyar Najeriya, gidan yaɗa labarai na Kaduna.
Yana da shekaru 81, ya bar mata biyu da ’ya’ya 14.
Za’ayi Sallar Jana’izarsa da misalin karfe 10 na safe a masallacin Juma’a na Jaafaru Estate, Kabala costain, Kaduna.