Daga Ibraheem El-Tafseer
Bayanan masu amfani da X da kamfanin ke shirin tattarawa sun haɗa da na hotunan fuskokinsu domin sabunta tsare-tsarensa na ba da kariya.
Duk mutanen da ke amfani da shafin na X na iya zaɓar hoton da suka ɗauki kansu da kuma katin shaida domin a tantance.
Tsarin ya kuma bayyana cewa X na iya tattara bayanai da suka shafi sirrin aiki da kuma karatun mutum.
Wannan na iya zama hanyar “tura muku gurabun aikin da aka tallata, da rabawa masu ɗaukar aiki idan ku ka nemi ayyukan”.
Akwai ma labarai da ke yawo da ke cewa kamfanin na X na shirin ɗaukar aiki ne.
Wasu rahotanni ma na cewa, a watan Mayun kamfanin na X ya mallaki wani kamfani mai ɗaukar ma’aikata da ake ƙira Lakie.
Wannan dai shi ne karon farko da kamafanin ya ɗauki wannan matakin tun bayan da Elon Musk ya sayi kamfanin Twitter a bara a kan dala biliyan 34.7.
Wannan sabon tsari zai soma aiki a ranar 29 ga watan Satumban 2023.
Kamfanin na X ya kuma shaidawa BBC cewa ‘Zai ba su zaɓin saka Katin Shaida (ID) nasu na aikin gwamnati tare da hoton da suka ɗauka da kansu domin tantancewa”.