Sauya ƙuɗi: Faɗa ya ɓarke a Legas

0
474

Faɗa ya ɓarke a wasu yankuna a kan babbar hanyar Legas zuwa Ikorodu a jihar Legas, kan karancin kuɗin sabbin Naira da kuma wahalhalun da manufar ta jefa ‘yan Najeriya.

A safiyar ranar Juma’a ne dai wasu ɓata gari da ake wa laƙabi da ‘yar Ariya Boys a unguwar Mile 12 da Ketu da Ojota da ke kan titin Ikorodu suka kai farmaki kan matafiya tare da haifar da hargitsi.

Wani direban mota da baya son a buga sunansa saboda fargabar tsangwama, ya ce sai da ya koma ɗaya daga cikin tituna saboda hargitsin ya sauya hanya.

An cigaba da tada hargitsin ayankin tare da jin karar harbe-harbe.

A halin da ake ciki, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da tashin hankalin da ke faruwa a yankin Mile 12 na jihar Legas.

Ya bayyana hakan ne ta shafin sa na Twitter a ranar Juma’a.

KU KUMA KARANTA:Yadda ƙarancin naira ya haddasa rikici a Ogun

Da yake mayar da martani ga wani sakon Twitter da ya nemi PPRO ya tabbatar da jita-jita, Hundeyin ya amsa, “Gaskiya ne. Mutanenmu suna can. An tura sassan ƙarfafawa. A zauna lafiya a can yayin da muke sa ido sosai da sarrafa lamarin. “

An kuma sami hargitsin a wasu sassan unguwar Agege sai dai wakilinmu ya shaida cewa zuwa yanzu ƙurar ta lafa.

Leave a Reply