Saudiyya ta gayyaci shugaban Iran Ra’isi

1
494

Daga Ibraheem El-Tafseer

Ƙasar Saudiyya ta gayyaci shugaban ƙasar Iran da ta daɗe tana adawa da shi domin ya ziyarci ƙasar.

Ministan harkokin wajen Saudiyya Faisal bin Farhan ne ya bayyana hakan bayan wata ganawa da ya yi da takwaransa na Iran Hossein Amir-Abdollahi a birnin Riyadh.

Ƙasashen biyu sun goyi bayan ɓangarorin da ke adawa da juna a rikice-rikicen gabas ta tsakiya, amma sun amince da daidaita dangantakarsu a watan Maris.

Akwai gagarumin bambancin ra’ayi tsakanin ƙasashen biyu,sai dai sun yanke shawarar daidaitawa da juna bayan da suka fahimci suna tafka asarar biliyoyin kuɗaɗe a yaƙin Yamen da sauran sassan gabas ta tsakiya.

Saudiyya ta yanke hulɗa da Iran a cikin shekara ta 2016, bayan da masu zanga-zanga suka mamaye ofishin jakadancinta da ke Tehran.

1 COMMENT

Leave a Reply