Saudiyya ta ƙira taron gaggawa na ƙasashen OIC, kan yaƙin Isra’ila da Hamas

0
270

Yariman Saudiyya Salman bin Abdulaziz ya ƙira taron gaggawa na ƙasashe mambobin ƙungiyar haɗin kan ƙasashen musulmi OIC.

OIC ita ce ƙungiya ta biyu mafi girma bayan Majalisar Ɗinkin Duniya da ke da ƙasashe 57 ciki har da Najeriya, ta bazu a nahiyoyi huɗu. Ƙungiyar ita ce muryar gamayya ta al’ummar musulmi.

A cewar wata sanarwa da aka buga a shafin intanet na OIC a ranar Lahadi, an shirya taron ne a ranakun 18 da 19 ga Oktoba a Jeddah, Saudi Arebiya.

An ƙira taron gaggawar ne domin tattauna rikicin da ke faruwa a zirin Gaza tsakanin Hamas da Isra’ila.

Leave a Reply