Saudiyya na son fara shigar da naman shanu da waken suya ƙasarta daga Najeriya

0
93
Saudiyya na son fara shigar da naman shanu da waken suya ƙasarta daga Najeriya

Saudiyya na son fara shigar da naman shanu da waken suya ƙasarta daga Najeriya

Ministan Harkokin Noma na Najeriya Mohammad Abubakar ya ce Saudiyya ta nuna sha’awar fara shigar da ton 200,000 na naman shanu da ton miliyan ɗaya na waken suya cikin ƙasarta duk shekara daga Najeriya.

Minista Mohammed ya shaida wa manema labarai a ranar Alhamis a Abuja cewa Saudiyya ta nuna sha’awar hakan ne bayan da Ministanta na Harkokin Noma ya ziyarci Najeriya tare da yin wasu taruka da ‘yan kasuwa a fannonin noma.

“Nuna sha’awar tasu kan wannan batu ke da wuya sai muka fitar da wani tsari da za mu iya samar da yawan abin da suke so da kuma biya musu buƙatarsu,” a cewar Ministan Harkokin Noman na Najeriya.

KU KUMA KARANTA: Masu sana’ar sayar da tumatur sun yi barazanar daina kai wa jihar Legas

Ya ƙara da cewa dama Najeriya na neman abokan hulɗa na kasuwanci don samun kuɗaɗen ƙasashen waje bayan da ta sha fama da ƙarancin dalar Amurka, lamarin da ya yi mummunar illa kan tattalin arzikinta da kuma rage darajar kudin ƙasar na Naira sosai.

Najeriya ta daɗe tana son raba ƙafa kan harkokin fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje, maimakon fitar da ɗanyen man fetur kawai, wanda a yanzu fitar da shi shi kaɗai ba ya iya riƙe tattalin arzikinta sosai.

Leave a Reply