Sanyi da hazo a Kano, ya sa jama’a da dama ba su fito harkokinsu ba

0
45
Sanyi da hazo a Kano, ya sa jama'a da dama ba su fito harkokinsu ba

Sanyi da hazo a Kano, ya sa jama’a da dama ba su fito harkokinsu ba

Daga Jamilu Lawan Yakasai

A safiyar wannan rana ta Lahadi Al’ummar Jihar Kano sun tashi cikin yanayin sanyi da hazo, wanda hakan ya janyo rashin hada-hadar su ta yau da kullum kamar yadda suka saba.

Sakamakon Jihar Kano jihace ta kasuwanci da hada-hadar al’umma naciki dama wanda suke makwabtaka da Jihar, lokacin da wakilin Neptune Jamilu Lawan Yakasai ya shiga gari domin gani da idanunsa, ya hadu da wani bawan Allah wanda ya fito da matarsa da dansa domin yiwa yaron “Shayi/Kaciya” sun iske wajen a rufe

Wanda dole sai da suka dauki lambar wayar daya rubuta a bakin shagon suka kira sannan yazo, da wakilin na Naptune yake tambayar mai shagon kodaman baya fitowa da wuri? Sai yace yanayin hazo da sanyi ne suka sanya ya makara bai fito ba.

KU KUMA KARANTA:Nan da shekarar 2035 za a kawar da cutar tarin fuka a Najeriya – Remi Tinubu

Gidajen mai da wasu muhimman wurare suma basu bude wuraren nasu ba, haka suma masu ababen hawa da suke sammakon fita suma basu fita ba,

Dr Munzali Muhammad likitane a asibitin yara na Hasiya Bayero, ya shawarci iyaye wajen kula da lafiyar yaransu, musamman wajen sa musu kayan sanyi da safar kafa data hannu, dama rashin yi musu wanka akoyaushe domin gujewa kamuwa da cutar mura da makamancinsu, ya kuma shawarci jama’a da surunga sanya takunkumin hanci domin gujewa daukar cuta.

Leave a Reply