Sama da rabin jama’ar Sudan na buƙatar agajin jinƙai – MƊD

0
232

Kusan watanni bakwai bayan soma yaƙi tsakanin sojojin Sudan da kuma rundunar RSF, rikicin ya sa sama da rabin jama’ar ƙasar na buƙatar agajin jinƙai, wanda hakan ya sa ake fargabar za a iya sake shiga halin da aka shiga a lokacin yaƙin Darfur shekaru 20 da suka gabata.

“Abin da ke faruwa yana da nasaba da mummunar mugunta,” in ji jami’ar kula da ayyukan jinƙai ta Majalisar Ɗinkin Duniya a Afirka a ranar Juma’a.

Sudan ta shiga ruɗani tun bayan da aka soma yaƙi a tsakiyar Afrilun bana, a lokacin da aka soma takun saƙa wadda ta zama babban rikici tsakanin shugaban sojojin na Sudan Janar Abdel Fattah al- Burhan da kuma kwamandan rundunar Rapid Support Forces wato Janar Mohamed Hamdan Dagalo.

Sai dai Clementine Nkweta-Salami, wadda ita ce shugabar tsare-tsaren ayyukan jin kai ta Majalisar Ɗinkin Duniya a Sudan, ta shaida wa wani taron manema labarai na Majalisar Ɗinkin Duniya cewa “yanayin ya munana kuma yana da daga hankali” kuma “a gaskiya, muna da ƙarancin kalmomi da za mu bayyana munin abin da ke faruwa.” Ta jaddada cewa “Rikicin Sudan ya yi munin da irinsa kaɗan ne a duniya”.

KU KUMA KARANTA: MƊD ta koka kan yadda matsin rayuwa ke ƙara tsanani a Sudan

Ta ce ana ci gaba da gwabza faɗa duk da cewa ɓangarorin da ke gaba da juna sun rattaɓa hannu kan wata yarjejeniya bayan tattaunawar zaman lafiya a Jeddah da ke ƙasar Saudiyya, inda suka yi alƙawarin kare fararen hula tare da samar da agajin jin ƙai ba tare da tsangwama ba ga mutane miliyan 25 da ke buƙatar taimako.

Janarorin da ba sa ga maciji da juna sun amince su kama wata gidauniyar jin ƙai, tare da haɗin gwiwar Majalisar Ɗinkin Duniya, in ji Nkweta-Salami. Haka kuma bayan taron a ranar Litinin, Majalisar tana fatan janarorin su aiwatar da abubuwan da suka yi alƙawari a Jeddah.

Ta bayyana cewa ɓangaren lafiya na ƙasar – wanda sama da kaso 70 cikin 100 na ɓangaren na wuraren da ake rikici ba su aiki – inda majalisar ta nuna damuwarta sakamakon ɓarkewar cutar kwalara da maleriya da bakon dauro.

Abin da muka gani tana ƙaruwa ita ce yunwa,” in ji Nkweta-Salami, da kuma tsantsan rashin abinci ga yara.

Majalisar Ɗinkin Duniya na son tallafa wa kusan mutum miliyan 12 – wato kusan rabin waɗanda suke neman agaji. Sai dai buƙatar da majalisar ke da ita na kusan sama da dala biliyan 2.6 na agajin jinƙai a Sudan a 2023 kusan kaso ɗaya bisa uku ne kawai aka samu, inda Nkweta-Salami ta buƙaci aka ƙara samar da ƙarin kuɗi.

Leave a Reply