Masu garkuwa da mutane na neman naira miliyan 10 domin su sako babban limamin al’ummar Uso a ƙaramar hukumar Owo ta Jihar Ondo, Alhaji Ibrahim Oyinlade da aka yi garkuwa da su ranar Asabar.
An bayyana cewa malamin yana aiki a gonarsa ne wasu ‘yan bindiga suka kai shi wani wuri da ba a sani ba.
Wata majiya daga iyalan ta bayyana cewa masu garkuwan sun tuntuɓi iyalan ne a ranar lahadi inda suka buƙaci a biya su kuɗin fansa naira miliyan 10.
“Sun tuntuɓi iyalan ne a ranar Lahadi inda suka buƙaci a ba su kuɗi naira miliyan 10.
KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da babban Limami a jihar Ondo
Wannan ita ce tattaunawa ta ƙarshe da suka yi da dangin.”
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Misis Funmilayo Odunlami, wadda ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce tuni mutanen rundunar da ‘yan banga suka shiga daji suna neman wanda abin ya shafa.
“DPO (na sashin ‘yan sanda na Uso) da mutanensa tare da ‘yan banga na cikin daji har yanzu don gano inda mutumin (wanda aka kama) yake,” in ji PPRO.
[…] KU KUMA KARANTA : Sai an bamu miliyan 10 za mu sako limamin Ondo – Masu garkuwa da mutane […]