Sabon ƙudurin sabunta haraji a Najeriya, zai yiwa arewa naƙasu – Masharhanta
Masu sharhi na fargabar illar da amincewa da sabon ƙudurin dokar haraji da shugaba Bola Tinubu ya turawa majalisar dokoki zai haifar.
Ƙudurin ya kai matakin karatu na biyu a majalisar dattawan ƙasa, lamarin da ke nuna yiwuwar amincewa da shi.
Kudurin mai sassa hudu ya hada da rabon kudin harajin da ake tarawa ga jihohi bisa yanda a ke samun kaso daga jihohin.
KU KUMA KARANTA:Ba a tsara ƙudirin sauye-sauyen haraji domin tauye arewa ba – Fadar Shugaban Najeriya
Wakilin Muryar Amurka a Abuja Nasiru Adamu El-Hikaya, ya tattauna da tsohon dan majalisar dattawa Ahmed Babba Kaita, wanda ya ce akwai sassa masu ma’ana a kudurin amma yankin arewa ka iya samun kalubale sannan “wasu jihohi kawai a kudancin kasar nan su za su fi cin moriya; ba zai zama adalci ba kai ka na sarrafa abu ka na kawo shi Kano ko Katsina ko Sokoto ka sayar, harajin da a ka samu a tattara a kai kudu, wannan ba adalci ba ne”
Shi kuma Garba Akoma Gona, dan jam’iyyar APC yana daga masu matukar hamaiya da kudurin, da yake yiwa wakilin namu bayani, ya ce matukar ‘yan majalisa su ka bari karatun kudurin ya tsallake, APC zata iya samun matsala a zabe mai zuwa a shekarar 2027 “ba shi da alfanu kuduri ne na durkusar da arewa. Laifin da PDP ta yi a zamanin Jonathan bai kama kafar ko farcen wannan ba.”