Saboda na ƙi amincewa Akpabio ya yi lalata da ni, shi ne dalilin da ya sa ya tsane ni – Sanata Natasha

0
17
Saboda na ƙi amincewa Akpabio ya yi lalata da ni, shi ne dalilin da ya sa ya tsane ni - Sanata Natasha

Saboda na ƙi amincewa Akpabio ya yi lalata da ni, shi ne dalilin da ya sa ya tsane ni – Sanata Natasha

Daga Ibraheem El-Tafseer

Ƙiyayyarsa da ni ta fara ne a watan Disamba lokacin da nake murnar zagayowar ranar haihuwata, wanda shi ma a lokacin yake murnar cika shekara (kusan ranar haihuwar mu ɗaya), da shi Sanata Akpabio.

Mun haɗu ne ni da mijina a wani yammaci a gidansa dake Akwai Ibom ya riƙe hannuna ya ce, na zo ya nuna min tsarin gidansa.

Na bi shi muna tafe yana nuna min shi kuma mijina yana bin mu daga baya yana waya, har muka zo a wani karamin falo muka zauna.

KU KUMA KARANTA:APC na daf da karɓar jiga-jigan NNPP ciki har da ‘yan majalisa – Ganduje

Sai Sanatan ya dube ni yace min, shin gidan nan ya burge ki? Na ce masa, Sosai gidan ya tsaru Gwanja shaawa. Anan ya buda Baki yace, min ko zan samu lokaci mu zo nan mu huta ni dake kawai? A lokacin da ya fadi haka mijina yana dan nesa damu. Sai na juya na kalli mijina in gani ko yaji. Shima Shugabana Majalisar da na kalli fuskarsa naga alamar Tsoron Kar azo mijina yaji.

Anan dai muka bar gidan, da dare mijina yayi ta tambaya ta Akan me Sanata yace, min naki gaya masa domin na San Yanda yake daukar Sanata da Muhimmanci Kuma Gashi za a yi bikin murnar haihuwata bana so na bata farin cikin.

Wannan na daga cikin dalilan da yasa Sanata ya fara kyara da hantara ta a Majalisa.

Kamar yadda Sanata Natasha ta fada a hirar ta da gidan talabijin na Arise

Leave a Reply