Saboda matsalar tsaro, mutanen Jibiya sun fara sare bishiyoyin kan hanya

0
200

A wani mataki na kare kansu daga ƙalubalen tsaro, mutanen ƙaramar Hukumar Jibiya da ke jihar Katsina sun fara sare bishiyoyin manyan hanyoyin shiga garin.

Sun ce sun ɗauki matakin ne domin samar da sarari ganin cewa ’yan bindigar daji na amfani da duhun bishiyoyin wajen tare motoci suna shiga daji da su.

Alhaji Surajo Agaji, ɗaya daga cikin ’yan ƙungiyar da ke aiwatar da aikin ya shaida wa manema labarai cewa, sun ɗauki matakin ne domin bayar da ta su gudunmuwar ta fuska tsaron yankin.

Ya kuma sha alwashin cewa aikin ba zai tsaya a iya hanyar Jibiya zuwa Katsina ba, dukkan hanyoyin shiga garin muddin suna da duhun itatuwan bakin hanya sai sun sare su.

KU KUMA KARANTA: Za mu inganta tsaro ta hanyar haɗa kan jami’an tsaro da tattara bayanan sirri

“A yanzu mun kashe sama da naira dubu 200 don gudanar da wannan aiki. Acikin kuɗin ne muka biya kuɗin hayar injin mai yankan itace, sayen ruwa da ɗan abincin da masu aikin za su ci, biyan motar da ke tafiya da mu da sauransu.

“Yanzu haka, daga cikin waɗannan kuɗaɗe ina jin bai wuce naira 5,000 ba a hannu sannan ga aikin yanzu ma aka fara yin shi.

“Bisa wannan ne muke neman gudunmuwar al’umma don ganin mun kammala wannan aiki wanda tuni aka fara ganin fa’idar shi,” in ji Alhaji Surajo.

Leave a Reply