Rundunar ‘yansandan Kaduna ta gano alburusai 210 na ƙirar 7.56MM a hanyar Zariya zuwa Funtuwa

0
117
Rundunar ‘yansandan Kaduna ta gano alburusai 210 na ƙirar 7.56MM a hanyar Zariya zuwa Funtuwa
Alburusai da aka kama

Rundunar ‘yansandan Kaduna ta gano alburusai 210 na ƙirar 7.56MM a hanyar Zariya zuwa Funtuwa

Daga Idris Umar Zaria

Rundunar ‘yansandan jihar Kaduna ta gano Alburusai 210 ƙirar 7.56mm a kan hanyar Zariya zuwa Funtua bayan wasu fasinjojin mota sun jefa wata jaka da ke ɗauke da kayan cikin matafiya.

Wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, DSP Mansur Hassan, ya fitar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Talata, 25 ga Nuwamba, 2025, lokacin da DPO na Samaru ya samu rahoto daga jama’a cewa fasinjojin wata mota kirar Volkswagen Golf mai launin baƙi sun jefa wata jaka da take da ban shakku a kusa da Dogon Icce, Samaru, Zariya.

Jami’an ‘yan sanda daga ofishin Samaru suka isa wurin da gaggawa, inda suka tarar da jakar da aka jefar. Bayan dubawa, sun gano Alburusai 210 7.56mm.

Bayan gano kayan, DPO ya sanar da sauran DPOs da ke kan hanyar zuwa Funtua domin yiwuwar cafke motar da mutanen da ke cikinta. Sai dai ba a kama su ba sakamakon jinkiri wajen samun bayanin farko.

KU KUMA KARANTA: Sojoji a Zamfara sun kashe ‘yan bindiga bakwai, sun ƙwato alburusai da dama

Rundunar ta yi zaton fasinjojin motar sun gane haɗari ne saboda yawaitar sintiri da tsauraran binciken motocin da ake gudanarwa a jihar.

Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kaduna, CP Rabiu Muhammad, ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da kasancewa masu lura da kuma ba da bayanai cikin lokaci ga jami’an tsaro. Ya tabbatar cewa an fara cikakken samame don kama mutanen da suka gudu, kana ya nanata kudirin rundunar na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Kwamishinan ya kuma gargadi duk masu aikata laifi da su guji shiga jihar ko su fuskanci fushin doka.

Leave a Reply