Rundunar ‘yansanda ta nuna damuwa kan ƙaruwar laifukan kisan kai a Kano

0
61
Rundunar 'yansanda ta nuna damuwa kan ƙaruwar laifukan kisan kai a Kano

Rundunar ‘yansanda ta nuna damuwa kan ƙaruwar laifukan kisan kai a Kano

Rundunar ‘yansanda ta jihar Kano ta nuna damuwa kan ƙaruwar aikata laifukan kisan-kai da kuma mutuwa a ruwa.

Kakakin rundunar, SP Haruna Ibrahim Kiyawa, ya ce a baya-bayan sun samu ƙaruwar aikata kisan-kai yayin faɗace-faɗacen daba ta hanyar amfani da wuƙa da kuma rasuwar mutane a ruwa.

Saboda haka rundunar ta yi gargaɗi ga al’umma bayan rahotannin yawaitar kisa da ta ce tana yawan samu a jihar.

A cikin gargaɗin da ta yi, rundunar ‘yansandan ta Kano ta shawarci al’ummar jihar da ma baƙin da ke shiga su kaffa-kaffa a al’amuransu na yau da kullum, saboda akwai ƙorafe-ƙorafen ayyukan kisan kai da dama da ta samu.

Dalilin haka ya ce, rundunar ƴansandan ta umarci jama’a su kara sanya ido da kuma sanar da hukuma mafi kusa a duk lokacin da suka ga wani al’amari da ba su amince da shi ba.

Cikin wata sanarwa da rundunar ƴansandan ta fitar ta ce ta yi nazari a kan ƙorafe-ƙorafen da ake samu na kisa, inda ta ce daga zarar faɗa ya ɓarke sai kawai wani ya cakawa wani wuka, sannan ana yawan tsintar gawa a wasu wurare.

”Wannan al’amari yana kai ga ana samun asarar rayuka sannan kuma yana sa alumma cikin damuwa ganin yadda suna rasa mutanensu” in ji SP Kiyawa.

KU KUMA KARANTA:Ba mu da labarin rasa rai a lokacin zanga-zanga – ‘Yan sandan Kano

Rundunar ƴansandan ta jihar Kano ta yi kira ga alumma a kan su kara sa ido musaman kan ƙananan yara da matasa tare da faɗakar da su a kan irin waɗannan matsaloli domin ganin cewa an ƙara kiyaye faruwar irin wadannan abubuwan.

A cikin gargaɗin, rundunar ta ce: ”A guji duk wani abu da zai haddada faɗa da wani ko haɗa jiki da jiki ko kuma duk wani rikici da zai kai ga ana yin fada” in ji shi.

Kwamishinan jihar Kano CP Dogo Garba ya yi kira ga duk wanda yake da bayanin faruwar irin wadannan abubuwa na faɗace-faɗacen da ke kai ga kisan kai da ya sanar da ofishin ‘yansanda mafi kusa don a yi gaggawar daukar mataki ta yadda za a kare rayuka da dukiyoyin alumma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here