Rundunar Sojin Najeriya ta gargaɗi masu neman a yi juyin mulki a ƙasar

0
149

Daga Ibraheem El-Tafseer

Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya gargaɗi masu ƙiraye-ƙirayen juyin mulki sakamakon matsin rayuwa, inda ya ce haƙuri abu ne mai muhimmanci a mulkin dimokuraɗiyya.

Janar Musa ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, yayin da yake ganawa da ‘yan jarida a birnin Fatakwal na jihar Ribas, bayan ƙaddamar da ayyukan wasu gine-gine.

Babban hafsan sojin ya buƙaci masu furta irin waɗannan kalamai da su daina.

An dai gudanar da jerin zanga-zangar nuna damuwa kan tsadar rayuwa a jihohin Kano da Oyo da Ogun a ƙasar ta Najeriya, yayin da mutane ke ci gaba da kokawa kan tsadar kayan masarufi.

KU KUMA KARANTA: DSS ta gargaɗi ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya a kan shirin zanga-zangar ‘tsadar rayuwa’

Najeriya na fama da hauhawar farashin kayan masarufi da sufuri da kuma ƙarancin kuɗaɗen shiga.

Bugu da ƙari darajar takardar kuɗin naira na ci gaba da zubewa idan aka kwatanta da dalar Amurka, wadda ke da matuƙar tasiri a ɓangaren tattalin arziƙi na ƙasar.

Ana dai ɗora alhakin wahalhalun da al’ummar ta Najeriyar ke fuskanta kan matakin shugaban ƙasar, Bola Tinubu na cire tallafin man fetur a ranar da ya karɓi mulki.

Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da sojojin Najeriya ke gargaɗin ‘yan ƙasar da ke ƙiraye-ƙirayen juyin mulki a ƙasar.

Leave a Reply