Rukunin farko na Alhazan jihar yobe za su dawo gida Najeriya

0
408

Daga Ibraheem El-Tafseer

A daren yau Talata, rukunin farko na mahajjatan jihar Yobe za su nufi jidda domin fara dawowa da su gida Najeriya. Kamar yadda ɗaya daga cikin mahajhatan wanda yana can ƙasar Saudiyya, Alhaji Muhammad Musa Kawuwale ya shaida wa wakilinmu.

Tun bayan sanarwa da ofishin hukumar Alhazan jihar Yobe ta fitar wadda ofishinta da ke birnin Makkah, ta sanar da alhazan cewa, kowane Alhaji ya fito da jakarsa wadda za ta ɗauki nauyin kaya kimanin kilo 32 a daren jiya.

Wadda za’a gwada kuma a tantance nauyin a hukumance kamar yadda hukumomin Saudiyya suka bayyana. Sannan sun ce da yammacin yau Talata kowane Alhaji ya yi ɗawafin ban kwana bayan Sallar La’asar.

KU KUMA KARANTA: Za mu nemi ƙarin kujerun hajji a shekara mai zuwa – NAHCON

Insha Allah yau da misalin ƙarfe 5:00pm na yamma za’a kwashesu a kai su Jiddah domin dawowa gida Najeriya bayan kwashe a ƙalla kwanaki 42 a ƙasa mai tsarki.

Muna roƙon Allah ya dawo dasu cikin iyalansu lafiya.
Allah ya sa sun yi aikin Hajji karɓaɓɓe.

Leave a Reply