An gano wasu ‘yan’uwa biyu da suka mutu sakamakon ruftawar wani gini a lamba 25, Ajao titin CWC, ta Olainukan Bus Stop. Ishawo. Ikorodu.
Ibrahim Farinloye, shugaban Hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa, (NEMA), ofishin kula da yankin, ta tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a ranar Asabar a Legas.
Mista Farinloye ya ce ’yan’uwan, Raƙib Atolagbe mai shekaru 7 da Mujib Atolagbe mai shekaru 9, sun maƙale ne a lokacin da wani shingen gidan da ke maƙwabtaka da su ya faɗa kan ginin nasu a lokacin da aka yi ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a ranar Asabar.
KU KUMA KARANTA: Mutum 2 sun mutu, an ceto 4, sakamakon ruftawar gini a Abuja
Ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:30 na safe. “Abin takaici ne cewa babu wani ƙiran gaggawa da aka yi amfani da shi yadda ya kamata ga waɗanda alhakin su ke da shi na ceton rayuka a lokacin da ya dace.
“A yanzu haka jami’an hukumar kula da gine-gine ta jihar Legas (LASBCA) suna nan a ƙasa domin tantance lamarin.
“Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta wa waɗanda suka rasu, ya kuma yi wa iyayensu ta’aziyya,” in ji Farinloye.
[…] KU KUMA KARANTA: Rugujewar gini ya kashe mutane biyu a Legas […]