Rikicin siyasa ta ɓarke a cikin gidan siyasar Kwankwasiyya

0
16
Rikicin siyasa ta ɓarke a cikin gidan siyasar Kwankwasiyya

Rikicin siyasa ta ɓarke a cikin gidan siyasar Kwankwasiyya

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Hakan na kunshe cikin wani dogon Sako da Daraktan Yada Labaran Gwamna Abba Kabir Yusuf ya wallafa a Shafinsa na Facebook.
Wasu naganin hakan danbace ta sanya zaren Siyasa tsakanin da da ‘dan Majalisar Tarayya na Rimin Gado, Toda da Dawakin Tofa wato Jobe.

Ga cikakken sakon daya wallafa kamar haka:

“Don Allah ku fadawa dan uwa na Hon. Jobe, idan fadan yake so dani to bisimillah, wallahi kodan bana tsoron sa. Kuma yafi kowa sanin haka.

KU KUMA KARANTA:A dakatar da batutuwan siyasa sai bayan Azumi – shugaban jami’iyar APC a Kano

Mutuncin sa a wajen na shine ya yiwa mutane abinda ya kamata, tun da akwai hakkin su a hannun sa, wallahi duk mutumin da mutane suka zaba to dolen sa ne ya sauke nauyin dake kansa.

Kada wani ya dauka wai ko ina son takara saboda haka zan juri wulakanci, ni dan halak ne, kuma na yadda da kaddara wallahi ya fi komai sauki in hakura da takarar wajen kare mutuncin al’ummar mu.

Takarar me? Kaine ka dauka sai da ita zaka rayu sai in fasa takarar kuma in yake ka tunda baka da shirin chanja hali.

 

Leave a Reply