Rayukan mazajenmu, ya fi mana jarumtakarsu

0
252
Rayukan mazajenmu, ya fi mana jarumtakarsu

Rayukan mazajenmu, ya fi mana jarumtakarsu

Daga Mairo Muhammad Mudi

Wani al’amari mai ban tsoron da ke faruwa a yanzun inda babu zato babu tsammani, sai ka ga maza suna tsaka-tsakin rayuwarsu ba tare da wata alama ba sun faɗi rigis sun ka sa miƙewa.

A cikin shekaru baya-bayan nan, mun ga yadda wasu maza masu lafiya da kuzari ke faɗuwa ba zato ba tsammani yayin gudanar da ayyukan motsa jiki. Wannan al’amari mai tayar da hankali yana ƙara yawaita, yana kawo mana baƙin ciki, hasarar rayuwa kan mazaje kai tsaye, tare da baƙin ciki a cikin al’umma.

Ba wai maza kaɗai irin wannan mutuwar fuju’a ke faruwa da su ba, amma har da mata sai dai na mazan ya fi rinjaye a zahiri.

Wasu shekaru nan baya wani abin baƙin ciki da har yanzu yana nan a raina. Wani ɗan’uwan maigidana, mutum ne dogo lafiyayye dan wasan ƙwallon kwando, ya kasance tauraron kwallon kwando wanda ke wakiltar jiharmu da kasarmu.

Duk wanda ya kalle shi zai ga lafiya ce ke tafiya ƙarara, tare da sha’awarsa saboda motsa jiki da ake gani ta ya ke yi a kowace yamma. Amma rashin sa’a ya afku a wata ranar Alhamis, inda ya fadi ba zato ba tsammani a filin wasa a lokacin yana azumi, bai sake motsawa ba haka muka rasa shi.

Haka nan, ƙaddarar Dr. Mahmoud Muhammad, tsohon babban likitan asibitin IBB Specialist kuma babban sakatare a Jihar Neja a da, ta girgiza al’umma. Bidiyo mai tayar da hankali ya nuna shi cikin kuzari, yana buga kwallo a filin ƙwallo kamar ƙwararren ɗan wasa. Amma cikin kiftawar ido, ya faɗi ƙasa, kamar yana hutawa cikin yanayi na gajiya, bai kuma tashi ba har abada.

KU KUMA KARANTA: Ana tuhumar wani ɗan Najeriya kan hana mata kai ƙarar mazajensu wajen ‘yansanda

Haka kuma, wani sanannen matashi ɗan Kannywood mai cike da kuzari, El-Muaz Muhammad, ya rasa rayuwarsa yayin da yake wasa da ƙwallo. Ya faɗi ba zato ba tsammani.

Irin waɗannan abubuwan bakin ciki yana ci gaba da yawaita. Wannan ya sa ni ke tambayar abin da ke haddasa waɗannan mutuwa masu ban mamaki a tsakanin mazajenmu majiya ƙarfi.

A matsayina na Musulma, na yarda da faɗin Allah S.W.T cewa, “Kullu nafsin za’ikatul maut” – “kowace rai za ta dandani mutuwa,” kuma ba wanda zai bar duniya kafin lokaci ya yi. Duk da haka, imaninmu ba zai taɓa cire mana alhakin kula da lafiyarmu ba.

Wadannan hasarar rayukan dole ne na yi kira mu farka, musamman ga mazanmu, waɗanda galibi ke sakaci da lafiyarsu cikin rashin kula, suna barin matansu zawarawa, marayu.

A al’ada, mun yarda da cewa mutuwa lamari ne da ba makawa, wanda aka kaddara zai faru a lokacin da Allah Ya ɗiba wa rai. Sai dai abin mamaki, yayin da muke ƙoƙarin jinkirta ko kauce mata, wasu daga cikin ayyukanmu na rashin sani sukan sa mu kusa da ita da gangan. Misali, muna kulawa da motoci da kyau kafin fara tafiya, hakanan ba za mu taba kwanciya a kan hanya ba saboda zai zama tamkar kisar kai ne.

Amma duk da haka, maza da yawa suna sakaci da jikinsu, ba tare da suna kula da shi yadda ya kamata ba, suna kai kansu ga haɗarin da ya kamata su gujewa.

A lokacin da nake aiki a ofishin jin kai na asibitin Suleja, na lura da bambanci mai ban mamaki. Ofishinmu yana kusa da dakin kula da masu ciwon hawar jini, inda na fara lura cewa galibin marasa lafiya mata ne.

Wannan ya sa na yi tunanin cewa mata sun fi maza samun hawar jini saboda damuwar da ke tattare da aure da rainon yara ga uwa. Amma daga bisani na gano gaskiyar cewa, yayin da mata suka fi zuwa neman magani in ba su da lafiya ko suna da juna biyu, maza sukan yi shiru, suna fama da rashin lafiyar don nuna jarumtaka har sai ya yi masu illa.

Maza su sani: mu danginku na buƙatar ku cikin koshin lafiya, bai kamata ku sadaukar da lafiyarku ku matsa wa kanku wajen aiki tuƙuru alhalin jikinku na son hutu.

Ku fara da yin gwaje-gwajen lafiyarku a kai a kai a asibiti ko a gida ma. Yanzun bature ya kawo mana sauƙi inda za ka iya sayen na’ura mai safara kanta cikin sauƙi na gwajin hawan jini da ciwon suga inda za su iya taimaka muku samun bayanan da za su sa ku yanke shawara ku ga likita nan take ko ku huta tukuna kafin motsa jiki mai tsanani ko zuwa wajen fama na yau da kullum. Ba na ce wannan ba zai maye gurbin shawarar likita ba, amma zai iya zama faɗakarwa mai amfani don neman taimakon gaggawa.

A takaice, ku kasance kuna cikin ƙoshin lafiya, ku huta yadda ya kamata, kuma ku kasance masu bayyanawa waɗanda kuka yarda da su matsalolin cikin matsaloli.

Akwai alamomin da jikinku zai faɗa muku lokacin da kuke buƙatar hutawa; ku yi na’am da wannan saƙon. Rayuwarku kyauta ce, kuma lafiyarku ba kawai na ku ba ce, har ma da waɗanda ke ƙaunar ku.

Mazaje a manta da jarumtaka a bai wa jiki haƙinsa. Ku huta in kun gaji, in jiki na maku ciwo a yi maza a ga likita. Ba mu fa buƙatar jarumtakarka, mun fi muƙatarku da rai da lafiyarku cas!

Mairo Muhammad Mudi
Za a iya tuntuɓar ta a mairommuhammad@gmail.com.

Leave a Reply