Rasuwar Saratu Giɗaɗo ta girgiza masana’antar Kannywood

1
193

Daga Ibraheem El-Tafseer

Da safiyar ranar Talata ne, labarin rasuwar fitacciyar jaruma a masana’antar Kannywood, Hajiya Saratu Giɗaɗo (Daso) ya karaɗe kafafen sadarwa. Hakan ya sa manema labarai suka yi zuzzurfan bincike, a ƙarshe dai ta tabbata Hajiya Daso ta rasu.

Ta rasu ne ba tare da ta yi jinya ba, har ma ta yi sahur na Azumin yau Talata. Inji makusantanta.

An haifi Saratu Giɗaɗo a ranar 17 ga watan Janairun shekarar 1968 a unguwar Chiranchi da ke ƙaramar hukumar Gwale da ke birnin Kano.

Margayiyar ta na daga cikin fitattun ‘yan wasan Hausa da suka shahara a fagen wasa.

Hajiya Daso dai Allah bai taɓa ba ta haihuwa ba, sai dai ‘ya’yan dangi da marayu da kuma almajirai da ta ke riƙe da su. Ko a jiya ma sai da ta yi bidiyo tana roƙa wa marayu da almajirai kayan sallah. Waɗanda take ƙiransu da ‘yan dugui-dugui ɗin Daso.

Ta rasu a yau Talata tana da shekaru 56 a Duniya. Kuma an yi jana’izarta kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.

1 COMMENT

Leave a Reply