Rashin ‘yansanda ba zai hana gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a Ribas – Fubara

0
55
Rashin 'yansanda ba zai hana gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a Ribas - Fubara

Rashin ‘yansanda ba zai hana gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a Ribas – Fubara

Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara ya bayyana mamakinsa game da zargin ‘yansanda da yunƙurin mamaye harabar hukumar zaɓen jihar (RSIEC) da nufin kawo cikas ga zaɓen ƙananan hukumomin da ake gudanarwa a yau Asabar.

A jawabinsa yayin wani taron manema labarai a fadarsa dake birnin Fatakwal a ranar Juma’a, gwamna Fubara ya ce yunƙurin ya zo da mamaki kasancewar ya samu labari a baya dake nuna cewar ‘yansanda na niyar janyewa daga zaɓen ƙananan hukumomin.

KU KUMA KARANTA:Wannan gobara ta tankar mai ta yi matuƙar kaɗa mu – Gwamna Fubara

Ya kuma yi tambayar ko mene ne dalilin da ya sa jihar Ribas ta fita daban, musamman abin da ya bayyana da sa ido mara tushe a kan hukumar zaɓen dake ƙarƙashin hurumin jiha.

Ya kara da cewar hukuncin kotun Abuja ya umaurci ‘yan sanda ne kawai da kada su samar da tsaro, amma ba wai su mamaye harabar hukumar zabe ta jihar ribas (RSIEC) ko kuma yin katsalandan a zaben ba.

A cewar gwamna Fubara, kamata yayi a baiwa hukuncin babbar kotun jihar Ribas fifiko, kasancewar shi aka fara bayarwa.

Leave a Reply