Rage farashin Gas na dafa abinci, ya jawo dogon layi a wuraren sayarwa a Kano
Daga Jamilu Lawan Yakasai
A daidai lokacin da al’ummar Musulmi suka fara azumin watan Ramadana, an wayi gari da cinkoson jama’a a gidajen sayar da iskar gas a birnin Kano, wanda hakan yake da alaka da sauƙin farashin da aka samu.
Gidajen sayar da iskar gas kamar kamfanin Ultimate Gas da AA Rano da ke Unguwar Sharada sun cika makil da jama’a, inda jama’a ke tururuwar sayen gas domin girki a lokacin azumi.
Wanda hakan ya janyo cinkosu matuka, da wakilin jaridar Neptune Prime a Kano Jamilu Lawan Yakasai yake zantawa da wasu da suka je siyan gas sun bayyana cewar, sun sami labarin cewar gas din ya sauka rugugu.
KU KUMA KARANTA:Gwamnatin Kano da haɗin gwiwar ‘yan kasuwa sun rage farashin kayan abinci
Sai dai a sanda sukace siya a cikin unguwanni su, sun sami farashin gas din akan kudi Naira 1,300 wani wajen kuma 1,250 akan kg1, hakan yasanya suka fito manyan kamfanoni domin kara samun sauki.
Da wakilin mu yake tambayar su ko akan nawa suka sami farashin gas din a manyan kamfanonin? Sai suka kada baki sukace sun zuba kg1 akan kudin da bai wuce 1,100 ba akan kg1.
Sai dai sunce dogon layi da suke bi suna shafe sama da awa 1 a wajen bayar da kudin gas, inda suke shafe sama da awa 2 a wajen dora gas.