Ra’ayi: Buɗaɗiyar wasiƙa zuwa ga Gwamnan Kano

0
180
Ra'ayi: Buɗaɗiyar wasiƙa zuwa ga Gwamnan Kano
Ali Sanni Munjibir

Ra’ayi: Buɗaɗiyar wasiƙa zuwa ga Gwamnan Kano

Daga Ali Sanni, Minjibir

Mai girma Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ina amfani da wannan damar domin kawo koken ‘yan’uwana ‘yan Kano. Ƴaƴanka masu karatu a makarantun gaba da sakandiri da ka taimaka ka biya masu kuɗin makarantarsu kamar yadda ka yi a shekarar da ta gabata.

Mai girma gwamna duk da tsarin rance da gwamnatin tarayya ta ƙaddamar yawancin ƴaƴanka da jikokinka na Kano har yanzu da yawa sun ka sa samun tallafin, musamman waɗanda suke a ƙauyuka saboda ƙarancin wayar da kai akan tsarin.

Mai girma Gwamna duba da yanayin da ake ciki na matsanancin tsadar rayuwa, biyawa ƴaƴan talakawa kuɗin karatu a wannan lokacin zai matuƙar taimaka masu.

KU KUMA KARANTA: Zanga-Zanga: An sa dokar hana fita a Kaduna da Zariya

Mai girma Gwamna nasan kai mai son ƴaƴan talakawa ne, don Allah ina mai maimaita roƙona da ka biyawa ƴaƴanka kuɗin makarantar su.

Ina maka fatan alheri.